Nijar: Ko an samu ci-gaba a batun tsaro?
March 23, 2026
Ayyukan ta'addanci a Jamhuriyar Nijar dai sun soma ne sosai a kusan shekara ta 2015, wanda ya kara ta'azzara sakamakon tabarbarewar tsaro a yankin bayan faduwar gwamnatin Libiya a shekarar ta 2011. An samu bullar kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Najeriya da kuma Mali, inda aka fuskanci manya-manyan hare-hare a yankunan Diffa da kuma Tillabery da suka janyo asarar rayuka da dama na sojoji da fararen hula gami da dukiyoyi masu tarin yawa.
Matsalar ta ragu
Sai dai ya zuwa yanzu duk da cewa matsalar ba ta kau ba, amma kuma a cewar Oumarou Kante da ke sharhi kan harkokin yau da kullum a kafar Internet a Jamhuriyar ta Nijar, ana iya cewa Nijar ta fi sauran kasashe makwabtanta tsaro. Ga masu sharhi kan harkokin tsaro da ayyukan ta'addanci kamar Farfesa Dicko Abdourahamane na jami'ar birnin Damagaram, kuwa ita harkar tsaro tana tafe ne da wasu ka'idoji wanda ake iya lissafin kaman batun sace mutane da garkuwa da su da ake gani a wasu kasashe ko kama wani yanki da sunan sansani na 'yan ta'adda.
Su kuwa kungiyoyin fararen hula kamar shugaban kungiyar SEDEL/DH Nijar Alhaji Baba Elmakiyya na ganin lalle akwai matsalolin tsaro a yankunan iyakoki a gabashi da kuma yammacin kasar ta Nijar, amma jami'an tsaro na taka rawar gani duk da cewa batu ne da ke da wahalar gaske. Sai dai kuma duk da raguwar manyan hare-hare a cikin 'yan shekarun nan, hari da 'yan ta'adda suka kai a daren 28 zuwa 29 ga watan Janairun 2026 a filin jiragen sama na birnin Yamai da yunkurin hari a filin jiragen sama na birnin Tahoua, ya sake mayar da hannun agogo baya.
Amma akwai sauran rina a kaba
Harin kuma ya kasancewa wata babbar dama ga su kansu hukumomin kasar da ma al'umma na sake tunani, domin fuskantar matsalar ta tsaro a kasar. Babban hafsan hafsoshin kasar ta Nijar Janar Sallau Barmu daga nashi bangare ya halarci wasu kauyuka a yankin jihar Tillabery, inda ya gudanar da shagulgullan karamar salla tare da al'umomin yankin da jami'an tsaro da ke ayyukan samar da tsaro a wani mataki na basu kwarin gwaiwa.