Kofin Duniya: Kanada ta haye, an yi waje da Afirka ta Kudu
June 29, 2026
Bayan shiga zagayen kif daya kwal na gasar cin kofin duniya ta bana na tantance kasashe daga 32 inda za a zabge rabi, a wannan Litinin ne kasar Jamus da ta lashe kofin sau hudu a tsawon tarihi za ta fafata da kasar Paraguay, wadda ita kuma sau biyu tana lashe kofin wasan kwallon kafa na duniya. Duk wacce ta samu nasara za ta tsallaka zuwa mataki na gaba na zagayen kasashe 16.
Tuni magoya baya musamman na kasashen Afirka ke ci gaba da da tsumayen rawar da kasashen da suka haye za su taka da ma kuma sauran kasashen duniya.
A cikin dare ake wasannin biyu, inda Jamus za ta kara da Paraguay, yayin da wasa na biyu kuma za a kara tsakanin tsakanin Netherlands da Maroko. Sannan gobe da Yamma Cote'dIvoire za ta kece raini da Norway, yin da daga bisani Faransa za ta fafata da kasar Sweden.
Ranar Laraba mai masaukin baki Mexiko da Ecuador za su yi wasa, sannan Ingila da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango za su gwada kwanhi. Daga bisani Beljiyam da Senegal za su yi wasa, a yayin da Amurka daya daga cikin masu masaukin baki za ta kece raini da Bosnia Hezegovina.
Ita kuma Spain za ta kara da Austria yayin da Potugal za ta tari Croatia. Su kuwa Switzerland da Aljeriya a ranar Jumma'a za su yi wasa, sannan daga bisani Australiya da Masar su yi wasa
Za a kammaka zagayen na kasashe 32 ranar Asabar da wasa tsakanin Ajentina da Cape Verde yayin da wanda da za a kara tsakanin Kwalambiya da Ghana zai kawo karshen tantance kasashe 16 da suka tsallaka zuwa mataki na gaba.
Tennis a Wimbledon: Kudi ko kwarewa?
Manyan 'yan wasan Tennis na duniya da ke karawa a wasan Wimbledon a Ingila sun kawo karshen nuna fusata da suke yi game da rashin jin dadin kudin da suke sumu a gasar mai tasiri a duniya. Shi dai wasan tennis na Wimbledon da ke karawa duk shekara na daga cikin manyan wasanni tennis na shekara-shekara a duniya.
Karkashin wasan tennis na Wimbledon a bangaren mutum guda na miji, duk wanda ya yi nasara zai samu kimanin kudi Pan-3,600,000 ,haka a bangaren mata na mutum guda, wanda haka yake nuna cewa duk bangorin biyu an kara kimanin 600,000 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Sannan a bangaren 'yan wasan biyu da suka yi nasara tare, a bangaren maza da na mata, kowanne zai samu 760,000 maimakon 680,000 a shekarar da ta gabata. Wannan wasan tennis na Wimbledon a Ingila an fara a ranar 22 ga wannan wata na Yuni kuma ana karewa ranar 12 ga watan gobe na Yuli.
Sabuwar bajinta a ninkayar mita 50
Fitacciyar 'yar wasan ninkaya ta Amurka mai suna Gretchen Walsh ta kafa sabon tarihi a wannan lahadi da ta gabata a wajen ninkayar mita-50, inda ta kammala cikin dakikoki 23 da motsi: Ia Gretchen Walsh ta kafa wannan tarihi a gasar da ke gudana a birnin Rome na kasar Italiya.