Koriya ta Arewa ta sake gwajin sabbin makamai masu linzami
April 14, 2026
Talla
Koriya ta Arewa ta sake gudanar da gwajin wasu sabbin makamai masu linzami, ciki har da masu kai hari daga teku, a matsayin gwajin sabon jirgin ruwanta na yaki mai suna Choe Hyon.
Rahotanni sun ce Shugaba Kim Jong Un ya halarci gwajin tare da manyan jami'an tsaro da suka hada da na rundunar sojin ruwa.
An harba makamai masu linzami da masu kai hari kan jiragen ruwa, inda rahotanni ke cewa sun kai hari kan wuraren da aka nufa cikin nasara.
Gwajin dai ya gudana ne a Tekun Yellow Sea da ke tsakanin China da yankin Koriya.