1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta hana Trump amfani da sojojin kar-ta-kwana

October 5, 2025

Kotu ta hana Trump aike wa da sojoji na musamman da ake kira National Guard domin murkushe masu zanga-zanga a Chicago.

https://p.dw.com/p/51VEm
Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Alex Brandon/AP Photo/dpa/picture alliance

Mai Shari'a Karin Immergut ta ce adadin tsirarrun mutanen da ke gudanar da zanga-zanga basu kai matakin amfani da karfin-tuwo wajen murkushe su ba, ta la'akari da korafe-korafen da aka shigar kotun na bukatar dakatar da shirin Mr. Trump na amfani da National Guard.

Karin bayani:Zanga-zanga na ci gaba da tsanani a Los Angeles na Amurka

Gwamnatin Trump ta daukaka kara kan hukuncin kotun tarayyar Oregon zuwa babban kotun daukaka kara da ke Circuit. Kazalika gwamnatin Trump ta kuduri aniyar aike wa da dakarun tsaro na musamman kimanin 200 zuwa 300 a jihohin da ke karkashin jam"iyyar adawa da Democrats domin kwantar da tarzoma wacce ta samu asali daga zanga-zangar Portland.

Karin bayani:An kama fiye da masu zanga-zanga 100 a Amurka

Mai magana da yawun fadar White House Abigail Jackson ta sanar da cewa Shugaba Trump yana da karfin ikon dakatar da zanga-zangar da ta rikide zuwa tashin hankali a Portland domin dakile hare-haren da masu boren ke kai wa kan kadarori da gine-ginen gwamnati.