Kungiyar Lititoci ta MSF ta dakatar da aiki a Gaza
September 27, 2025
Talla
Sanarwar ta zo ne bayan da sojojin Isra'ila suka matsa kaimi kan farmakin da suke kai wa nta sama da ta kasa ga mayakan Hamas, inda dubban Falasdinawa suka tsere daga matsugunnensu.
Jacob Granger jami'in kungiyar ta MSF ya ce an bar su da rashin zabi illa na su dakatar da ayyukansu yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kewaye asibitocin da suke aiki a ciki.
Hukumar kare fararen hula a Gaza ta ba da rahoton mutuwar mutane akalla 22 tun daga wayewar gari a Gaza.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Isra'ila ta fitar a ranar Juma'a ta ce sojojin sama sun yi luguden wuta kan wurare sama da 140 a duk fadin zirin Gaza, ciki har da maboyar mayakan Hamas dake karkashin kasa.
Karin Bayani:Jami'an agaji 192 sun halaka a zirin Gaza