1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Macron ya kai ziyara irin ta ta farko a Syria

July 6, 2026

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Damascus na kasar Syria. Ziyara irin ta ta farko daga Turai tun bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a shekarar 2024.

https://p.dw.com/p/5Gg8K
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al-Shaibani
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al-ShaibaniHoto: Ludovic Marin/AFP

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya isa birnin Damascus na kasar Syria, kamar yadda kamfanin dillancin labaran gwamnatin Syria ya bayyana. Wannan ita ce ziyara ta farko da wani shugaban kasa daga kungiyar Tarayyar Turai ya kai Syria tun bayan da 'yan tawaye karkashin jagorancin Shugaba Ahmed al-Sharaa suka hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a shekarar 2024.

Ana kallon ziyarar a matsayin wata alama ta sauyin siyasa da diflomasiyya da Syria ke fuskanta karkashin shugabancin Ahmed al-Sharaa, tsohon kwamandan kungiyar Al-Qaeda, wanda yanzu ya kulla kyakkyawar alaka da kasashen Yamma da na Gabas ta Tsakiya da a baya suka kaurace wa gwamnatin Bashar al-Assad, yayin da yake kokarin sake gina kasar bayan shekaru 13 na yaki.