Gabon na nazarin shafukan sada zumunta
February 26, 2026
Tun a ranar 17 ga watan Febrairu ne dai hukumar kula da kafofin watsa labarai ta dakatar da amfani da shafukan sada zumuntan, tana zargin abubuwan da aka wallafa a intanet da haifar da rikici da rarrabuwar kawuna a cikin al'umma.
Ya zuwa wannan rana ta Alhamis dai Facebook da TikTok, dandalin da aka fi amfani da su a Gabon, da kuma YouTube da Instagram har yanzu suna rufe, yayin da WhatsApp ke buduwa ya kuma rufe, ya danganta da kamfanonin waya.
TikTok ya tuntubi hukumar kwana guda bayan sanarwar, inda ta yi alkawarin kiyaye dukkan ka'idojin dijital, wanda ke girmama hakkoki da tsare mutuncin 'yan kasar ta Gabon," in ji kafofin watsa labarai na cikin gida.
Tsohon firaministan Gabon Alain-Claude Bilie-By-Nze, wanda yanzu haka yake cikin 'yan adawa, ya yi Allah wadai da haramcin kuma ya saba wa kundin tsarin mulki.