1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ci raniSpaniya

Tsibirin Canary: Makabartar 'yan ci-rani

Jan-Philipp Scholz LMJ
February 11, 2026

Tsallaka tsakanin yammacin Afirka da Tsibirin Canary, na zaman hanyar da ta fi lakume rayuka ga masu kokarin shiga Turai ba bisa ka'ida ba. Da dama na yi wa Turai kallon tudun mun tsira, tare da yin kasada da rayuwarsu.

https://p.dw.com/p/58WXF
Canary | Spaniya | Bakin Haure | Teku | Atlantic | Asarar Rayuka | Rikici | Kisan Gilla
'Yan ci-rani da dama na riskar ajalinsu a Tsibirin CanaryHoto: Europa Press Canarias/IMAGO

A wasu lokutan ma, a kan samu rikicin da ke janyo asarar rayuka. Bin hanyar Tekun Atlantic zuwa Turai daga yammacin Afirka ya ragu matuka, kamar yadda mahukunta suka bayyana. Kididdigar hukuma ta nunar da cewa, bakin haure sama da 40,000 ne suka shiga Turai a 2024, yayin da a bara suka ragu zuwa 18,000 kacal. Masu sanya idanu na alakanta hakan da hadin gwiwar da aka yi, tsakanin Turai da kuma kasashen Afirka da ke zaman hanyar da bakin hauren ke bi kamar Mauritania da Maroko da ma tsauraran matakai da wadannan kasashe suka dauka a kan iyakokinsu.

Asarar rayuka da samun rauni

Sai dai, rahotannin rikici har da kisa a yayin da masu shiga Turai ta barauniyar hanya ke cikin kwale-kwalensu na karuwa. Wasu fasinjoji da suka yi irin wannan kasada a shekara ta 2024, sun shaidar da yadda wasu maza uku daga Senegal suka ci-zarafin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalensu. A cewarsu, wasu da yawa sun ji ciwukan da sai dai su mutu da su. Ismael Outtara da iyalansa sun hau kwale-kwale daga Maroko, inda suka makale a Tekun Atlantic tsakanin kudancin Maroko da Tsibirin Tenerife tsawon kwanaki.

Cikin sa'o'i 24, 'yarsa mai shekara daya a duniya da matarsa suka rasu. Kamar dubban mutane, Ouattara da iyalansa sun baro Cote d'Ivoire da nufin samun rayuwar tudun mun tsira a Turai. Sai dai mafarkinsu bai cika ba, domin ya rasa matarsa da 'yarsa a teku shekaru hudu da suka gabata. A shekara ta 2025, 'yan sandan Spaniya sun cafke mutane 19 bayan da kimanin mutane 50 suka rasa rayukansu tsakanin Senegal da Tsibirin na Canaria. 'Yan sandan, sun zargi mutanen da tayar da hankula da kuma kisan gilla. Babu tabbacin ko wadanda aka kama mambobin kungiyoyin da ke safarar mutane ne, ko kuma suma fasinjoji ne.

Ba a iya hukunta masu aikata laifin

Rundunar 'yan sandan Spaniya ta ki cewa komai, yayin da DW ta tuntube rundunar domin karin haske. A lokuta da dama, ba wai kawai ba a hukunta mutanen da ke aikata muggan laifuka irin wannan ba ne, ba a ma biyan diyya ga iyalan wadanda aka halaka ko illata. Loueila Sin Ahmed Ndiaye lauya ce a Tsibirin na Canary, kuma tana lura da laifukan da aka aikata yayin rikici a kwale-kwale. Ta shaidawa DW cewa yana da wahala a hukunta wadanda suka aikata laifuka a tekun, kasancewar akwai iyaka a ikon da Spaniya ke da ita wajen bincikar kisan da aka aikata a tsakiyar teku.

A cewarta, bayanan da shaidu suka bayar da kuma rahotannin da 'yan sanda suka fitar, sun nuna cewa mutane na kidimewa. Sanyi da rashin tabbas da firgici a wasu lokutan, na shafar lafiyar kwakwalensu matuka. Ta kara da cewa yana da matukar wahala a samu bayanan da ake bukata, domin hukunta wadanda suka aikata laifin. Wadanda suka tsira ba sa bayar da hadin kai, kuma suna kin yin magana da 'yan sanda.