1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin al'ummar Agadez kan takaddamar ORANO

November 28, 2025

A Jamhuriyar NIjar, jama'a na ci gaba da tsokaci musamman a jihar Agadez kan takaddamar kamfanin Orano mai hakar ma'adanin Uranium da kuma gwamnatin NIjar.

https://p.dw.com/p/54SjQ
Kamfanin harkar ma'adanin Uranium na Orano a Arlit
Kamfanin harkar ma'adanin Uranium na Orano a ArlitHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Kamfanin ORANO mai aikin hakar ma'adanin Uranium a kasar Nijar shekaru da dama, a rana 27 ga watan Nuwamba na 2025 ya fitar da sanarwar cewa kasar Nijar ta fitar da Uranium malakin kamfanin ba tare da sanin ina aka kai ba, lamarin da ya sa al'umma da kungiyoyin farar hula baiyana ra'ayoyin su kan batun. 

Wannan aiki dai na hako Uraniun da kasar Faransa ta share shekaru tana yi, 'yan Nijar musumman 'yan jihar Agadez inda ake fitar da arzikin sun sha kokawa saboda basu taba cin gajiyar arzikin ba inji Djamila Oumar wata 'yar gwagwarmaya a jihar ta Agadez

Gamaiyar kungiyoyin jihar Agadez COSCRAZ a ta bakin magatakardarta Moussa Bilal ya ce ORANO ba ta da 'yancin sanin ina Nijar ta sayar da ma'adaninta domin kamfanin ya dade da ya zama malakin kasar Nijar