1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Masu Aikin Sa Kai Sun Mutu Sakamakon cutar Ebola a Kongo

May 23, 2026

Kungiyar agaji ta Red Cross ta sanar cewa wasu masu aikin sa kai uku sun mutu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo bayan sun kamu da cutar Ebola yayin gudanar da aiki a watan Maris.

https://p.dw.com/p/5EEhq
Ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross dauke da akwatin gawar wani mutum da ya mutu sakamakon cutar Ebola.
Ma’aikatan kungiyar agaji ta Red Cross dauke da akwatin gawar wani mutum da ya mutu sakamakon cutar Ebola.Hoto: Gradel Muyisa Mumbere/REUTERS

Kungiyar ta ce mutanen uku na aiki ne a garin Mongbwalu da ake ganin shi ne inda cutar tafi kamari. Sun kamu da Ebolan ne yayin aikin daukar gawarwaki a wani aikin jin kai

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ya zuwa yanzu an tabbatar da mutane 82 sun kamu da cutar a Kongo, yayin da mutane bakwai suka mutu. baya ga zargin akwai daruruwan mutane da suka kamu har ila yau.

Kungiyar Red Cross din ta ce har yanzu akwai damar dakile yaduwar cutar, amma lokaci na kurewa, yayin da ake ci gaba da wayar da kan al'umma kan yadda za su kare kansu daga cutar.