1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan sa kai sun yi kisan gilla a gabashin Kwango

Zainab Mohammed Abubakar
January 26, 2026

MDD da shugabannin kungiyoyin fararen hula sun ce maharan sun kashe sama da mutum 20 a harin baya bayan nan a Ituri.

https://p.dw.com/p/57Uu3
Hoto: Stringer/REUTERS

Mayakan sa kai nw kungiyar IS sun kashe akalla fararen hula 22 a wani kauye a lardin Ituri da ke gabashin Kwango, a cewar wani rahoto na ciki na Majalisar Dinkin Duniya da shugabannin kungiyoyin fararen hula na yankin, wanda shi ne hari na baya-bayan a yankin.

Rahoton MDD da Reuters ta gani ya ce maharan sun kai hari a Apakolu, kimanin kilomita 25 Arewa maso Yammacin Eringeti a yankin Irumu na lardin Ituri, da sanyin safiyar ranar Lahadi, kuma suka sace mutane da ba a san adadinsu ba.

Christophe ‌Munyanderu, shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta yankin da aka fi sani da CRDH ta Faransa, da ke da hedikwata a Irumu, ya ce an kashe fararen hula 25, ciki har da mutane 15 wadanda aka gano gawarwakinsu a cikin wani gida da kuma wasu bakwai a kan hanya.

An gano maharan a matsayin membobin rundunar ADF, wata kungiyar 'yan bindiga ta Yuganda da ke aiki a gabashin Kwango.