1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

MDD za ta yi taron gaggawa kan kisan fararen hula a Sudan

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 6, 2025

Kasashe fiye da 50 ne suka amince da taron karkashin jagorancin Burtaniya da Jamus da Netherlands, sai Norway da Ireland

https://p.dw.com/p/53Dao
Halin da 'yan gudun hijira daga birnin El-Fasher na Sudan suke ciki kenan.
Hoto: NRC/AP Photo/picture alliance

Hukumar kare hakkin 'dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya, ta shiya gudanar da taron gaggawa kan kashe-kashen da fararen hula ke fuskanta a birnin al-Fashir na kasar Sudan, bayan da 'yan awaren RSF suka kwace ikon yankin daga hannun sojoji.

Kasashe fiye da 50 ne suka amince da taron, karkashin jagorancin Burtaniya da Jamus da Netherlands, sai Norway da Jamhuriyar Ireland, wanda za a gudanar ranar 14 ga wannan wata na Nuwamba.

Karin bayani:Amurka ta kudiri aniyar kawo karshen yakin Sudan

Birnin al-Fashir na zama tungar karshe ta yankin Darfur da ta rage a hannun sojoji masu biyayya ga Janar Abdel Fattah al-Burhan, gabanin komawarsa hannun RSF da ke karkashin jagorancin Muhammad Hamdan Dagalo.

Yakin basasar Sudan na shekaru biyu da rabi, ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a musamman ma kananan yara da mata, tare da raba miliyoyi da gidajensu, wanda har yanzu aka gaza kawo karshensa.