Jamus ta yi kira kan rage goyon baya ga Ukraine
April 15, 2026
Pistorius ya bayyana hakan ne bayan wani taro da aka gudanar a birnin Berlin na kungiyar kasashe kusan 50 da suka hada kai wajen tallafawa Ukraine da kayan soji. A cewarsa halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya na amfanar da Rasha, domin hauhawar farashin mai na kara shigar da kudade cikin asusun yakin suhgaban Rasha Vladimir Putin.
Shi ma Ministan tsaron Birtaniya, John Healey, ya bayyana cewa jiragen yaki marasa matuka na taka muhimmiyar rawa a fagen daga inda ya bayyana kusan kashi casa'in da 6 cikin 100 na asarar da Rasha ta yi a watan Maris na da nasaba da wadannan jirage.
Ya kuma sanar da cewa gwamnatin Birtaniya za ta bai wa Ukraine jirage marasa matuka dubu 100 da 20 kafin karshen shekarar nan. Haka kuma ya yabawa tayin da Ukraine ta yi na taimakawa kasashen yankin Gulf wajen kare kansu daga hare-haren wadannan jirage da ma na makamai masu linzami daga Iran.