Ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuka a Kenya
March 7, 2026
Jami'an 'yan sandan Kenya sun ce wadanda suka gamu ajalinsu a ambaliyar ruwan sun nutse ne yayin da wasu kuma wutar lantarki ce ta ja su. Shugaban 'yan sandan yankin, George Seda ya yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa yayin da ake ci gaba da neman jama'a da ake kyautata zaton ruwa ya tafi da su.
Iftila'in ambaliyar ruwan ya faro ne daga daren ranar Juma'a zuwa wannan Asabar din, inda ya toshe hanyoyin tare da lalata ababen hawa fiye da 100. Ambaliyar ta kuma kawo tsaiko ga tashi da saukar jiragen sama, inda aka rika mayar da jirage zuwa birnin Mombasa.
Karin bayani:Ambaliya ta kashe mutane 70 a Kenya
Tuni rundunar sojin Kenyar ta tura da karin jami'an aikin ceto jama'a yayin da kungiyar Red Cross ta kasar ta ce ma'aikatanta na kokarin isa wuraren da mutane suka makale, sai dai kuma suna samun tsaiko sakamakon cunkuson hanya da kuma ambaliyar da ta sanya shiga wasu sassan ya yi wahala.