EU ta bayar da shawara kan zaben Najeriya
October 3, 2025
Hukumar Zaben Najeriya INEC da tawagar ta jami'an kungiyar Tarayyar Turai da suka sa ido a zaben kasar da aka yi a 2023, sun gudanar da tattauanawa ta musamman a kokarin kyautata zaben kasar da kan bar baya da kura. Jami'an kungiyar ta EU sun isa Najeriyar ne, domin bin ba'asin shawarwarin da suka bayar a kan zaben da aka gunara a 2023.
Matakan da ya kamata a dauka
Shawarwari 23 ne suka bayar da suke son ganin an dauka, domin kyautata zaben na Najeriya ta yadda zai kasance ya kai matsayi na kasa da kasa. Mr. Barry Andrews shi ne shugaban tawagar kungiyar ta EU, ya bayyana cewa: "Mun yi farin ciki da muka ga an samu ci-gaba wajen aiwatar da wadannan shawarwari da muka bayar, duk da cewa mun fahimci akwai karancin lokaci saboda wasu daga ciki na bukatar sauye-sauye ne na doka da na bangaren mulki da tsarin mulki wanda yake da wahala sosai....
Wadannan shawarari sun hada da, amincewa da jefa kuri'a kafin ranar zabe ga masu ayyuka na musamman da 'yan Najeriya da ke kasashen waje da sake nazarin zabubbukan da aka fusknaci takaddama. Kokari ne dai na gyara kayanka daga tawagar kungiyar Tarayyar Turan, a kan s zaben na Najeriya. Da alamun baki ya zo daya, tsakanin tawagar EU din da sauran kungiyoyi da ke saka idanu a zaben Najeriyar kamar kamar yadda manajan gudanarwa na kungiyar fara hula ta Yaiga Africa Paul James ya nunar.
Martanin Hukumar Zabe
Shugaban Hukumar Zaben Najeriyar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana halin da ake ciki, a kan shawarwarin da suka gabatar musamman wadanda suka shafi hukumar zaben: "A tsanake Hukumar Zabe ta duba takwas daga cikin shawarwarin da aka bayar da suka shafe ta, tuni mun dau mataki a kan sassan da ke bukatar sashen mulki na hukumarmu.........."
Wannan ce ziyara ta uku da tawagar masu sa ido daga kungiyar Tarayyar Turan suke kawowa Najeriya, tun bayan kammala zaben 2023 a kokarin ingatan tsarin zaben Najeriyar ya kai mizanin na kasa da kasa.