1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: INEC za ta yi wa Jam'iyyu 14 rajista

September 12, 2025

A Najeriya, bayan share tsawon lokaci ana kai kawo, hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta ce ta tantance wasu kungiyoyi na siyasa har 14 domin komawa zuwa jam'iyyun siyasa.

https://p.dw.com/p/50Q5b
Nigeria | INEC | Mahmood Yakubu I Shugaban hukumar zaben Najeriya
Nigeria | INEC | Mahmood Yakubu I Shugaban hukumar zaben NajeriyaHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

An dai dauki lokaci ana sa in sa bayan da wasu kungiyoyin siyasa har 171 suka nemi hukumar zaben INEC ta sahale musu rikidewa ya zuwa jam'iyyun siyasa a cikin tarayyar Najeriya, kafin wata sanarwar da a cikin ta hukumar ta ce 14 ne suka cancanta su zama jam'iyyun da za su taka rawa a fagen siyasar kasar.

INEC din dai ta sa kafa ta shure wasu bukatu 157 da ta ce basu cancanci rikidewa zuwa jam'iyyu ba.

Karin Bayani: Neman karuwar jam'iyyun siyasa a Najeriya

Mahmood Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya INEC
Mahmood Yakubu shugaban hukumar zaben Najeriya INECHoto: Emmanuel Osodi/imago images

Ana dai kallon sabon matakin da kokarin wankan tsarki a bangaren hukumar zaben da sannu a hankali ta ke dada fuskantar rikicin iya tantance bukatu cikin fagen siyasar tarayyar Najeriyar.

Sabbabin jam'iyyun dai sun hada da African Transformation Party, da All Democratic Alliance, da Advance Nigeria Congress da kuma Abundance Social Party.

Sauran sun hada da African Alliance Party da Citizens Democratic Alliance da Democratic Leadership Alliance da kuma Grassroots Initiative Party.

Karin Bayani:Ko hadakar jam'iyyun adawa ne mafitar Najeriya?

Jami'an hukumar zabe ta INEC a Najeriya
Jami'an hukumar zabe ta INEC a NajeriyaHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Akwai kuma Green Future Party da Liberations Peoples Party da kuma National Democratic Party. Sai kuma National Reform Party da Patriotic Peoples Alliance da kuma Peoples Freedom Party.

A ranar laraba ta makon gobe ne INEc din tace za ta kamala tantance takardun sabbin jam'iyyun da ma ganawa da shugabannin su na riko