1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNajeriya

Rufe makarantu ne mafitar Najeriya?

Aliyu Muhammad Waziri LMJ
November 24, 2025

Gwamnatin jihar Bauchi ta ba da umarnin rufe dukkanin makarantu a jihar tun daga matakin firamare da sakandare har zuwa manyan makarantu, domin kare rayukan dalibai da malamai da sauran ma'aikata.

https://p.dw.com/p/549YN
Najeriya | Tsaro | Makarantu | Dalibai | Hadari | Hari | 'Yan Bindiga | Garkuwa
Makarantu a Najeriya, sun jima suna tsintar kansu cikin harin rashin tsaroHoto: Afolabi Sotunde/Matrix Images/picture alliance

Gwamnatin jihar Bauchin ta bukaci al'umma, su yi hakurin bin umarnin da kuma kara sanya ido da sanar da jami'an tsaro duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba, domin ta haka ne za a samu damar shawo kan matsalar a kan lokaci har dalibai da malamai su koma makarantu.

Jihohi da dama sun rufe makarantu

Baya ga Bauchi a yankin na Arewa maso Gabas akwai jihohin Adamawa da Taraba, sai kuma Katsina a Arewa maso Yamma da kuma Plateau da jihar Niger a shiyyar Arewa ta Tsakiya da suka dauki irin wannan matakin sakamakon matsalolin tsaron bayan abin da ya faru a jihar Kebbi da Niger.

Ko kungiyar Miyetti Allah za ta je Amurka?

Ko da yake a kasa baki daya ma gwamnatin tarayya ta ma'aikatar ilimi karkashin darakta mai kula da manyan makarantun sakandare Binta Abdulkadir ta sanar da rufe makarantun sakandare na hadaka wato Unity Schools kimanin 41 a fadin kasar domin bai wa daliban kariya.

Rashin tsaro na fadada?

Wannan umarni na rufe makarantun na zuwa ne a daidai lokacin da wasu mahara suka kashe 'yan sanda biyar a karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi, lamarin da ya kara tabbatar da akwai matsalar tabarbarewar tsaro. Umarnin ya shafi har da makarantun gwamnatin tarayya da masu zaman kansu a daukacin jihar, kamar yadda sanarwar ma'aikatar ilimi ta bayyana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani