Najeriya ta fusata da kyamar baki a Afirka ta Kudu
May 3, 2026
Talla
Gwamnatin Najeriya ta gayyaci babban jami'in diflomasiyyar Afirka ta Kudu a Abuja, sakamakon hare-haren da ake kai wa 'yan kasashen waje a kasar.
Afirka ta Kudu dai ta dade tana zama mafaka ga ma'aikatan Afirka, amma tana fama da rashin aikin yi da ya haura kashi 30 cikin 100.
An sha samun zanga-zangar nuna kiyayya ga mutanen ketare a Afirka ta Kudun, ciki har da sabbin rikice-rikicen da suka barke a makonnin baya.
Matakin Najeriya ya biyo irin wanda Ghana ta dauka, inda ta gayyaci wakilin Afirka ta Kudu a Accra kan zargin hare-hare ga 'yan kasarta.
Afirka ta Kudu dai ita ce kasar da ta fi bunkasar masana’antu a nahiyar Afirka, kuma sama da mutane miliyan uku ’yan kasashen waje ke zaune a cikinta, kusan kashi 5.1 cikin 100 na yawan jama'arta.