1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO na nazarin hanyoyin dakile barazanar kutsen Rasha

October 15, 2025

Kasashen kungiyar tsaro ta NATO na tunanin yin katagar karfe kafin shekarar 2027 domin bullo wa kalubalen kutsen sararin samaniya da Rasha ke yi wa wasu kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/523sF
Taron ministocin tsaron kasashe membobin NATO
Taron ministocin tsaron kasashe membobin NATOHoto: IMS/NATO

Ministocin tsaro na kasashe membobin kungiyar NATO sun gana a birnin Brussels a wannan Laraba inda suka tattauna hanyoyin karfafa goyon bayan da suke bai wa Ukraine da kuma inganta matakan yin martani ga Rasha bayan kutsen da ta yi wa sararin samaniyar wasu kasashen Turai da jirage maras matuka.

Sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth wanda ya kasance a gurin taron ya karfafa gwiwa ga kasashen Turai da Canada kan matakin da suka dauka na kara tallafawa Ukraine a karkashin shirin Purl wanda Washington ta samar domin bai wa Kiev damar sayo makamai kirar Amurka.

Karin bayani: Jamus ta yi gargadin yuwar shiga yaki kai tsaye tsakanin Rasha da NATO

Sai dai babban batu da ya fi daukar hankali a taron shi ne yadda za a tunkari barazanar jirage maras matuka na Rasha, kuma kan wannan batu ministocin tsaron kasashen Turai da tun tuni da suka ba da shawarar yin kantagar karfe za su gana da maraicen yau inda za su duba karin wasu matakai.