1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

NATO ta yaba wa yunkurin Trump na sulhu a Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
November 27, 2025

Sakataren kungiyar kawancen tsaro ta NATO Mark Rutte ya yaba wa yunkurin shugaban Amurka Donald Trump na kawo karshen yakin Ukraine, yaki mafi muni a nahiyar Turai tun bayan yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/54PDG
Ganawa tsakanin Trump da sakataren kungiyar NATO Mark Rutte a Washington
Ganawa tsakanin Trump da sakataren kungiyar NATO Mark Rutte a WashingtonHoto: AFP

Mark Rutte ya ce an sa himma sosai wajen kokarin yin sulhu a yakin Rasha da Ukraine a saboda haka ina gode wa shugaba Trump kamar yadda ya shaida wa yan Jarida a ziyararsa zuwa Iceland.

Shawarar tsagaita wutar ta sami tagomashi yayin da tattaunawa ta kankama tsakanin Jami'an Rasha da Ukraine da Washington da kuma na tarayyar Turai inda aka yi tattaunawa a Geneva da kuma Abu Dhabi.

Amurka dai ba ta wallafa sabon jadawalin shawarwarin ba, sai dai Trump ya ce an yi masa kwaskwarima daga shawarwari 28 da ya zayyana tun da farko wanda Kiev da aminanta na Turai suka ce sun karkata ga Kremlin.