Nijar: kotu ta tura tsohon minista kurkuku bisa zargin fyade
January 8, 2026
A ranar Talata 06.01.2026 ne aka gurfanar da Pr Mamoudou Djibo, tsohon ministan ilimi mai zurfi na kasar Nijar kana shugaban makaranta mai zaman kanta "Lelite" a gaban kotun birnin Yamai ,a bisa zargin da wata dalibarsa ta yi masa na cewa ya yi mata fyade.
Bayan da alkali mai bincike ya saurari tsohon ministan dan kimanin shekaru 70 a duniya ne, ya tuhume shi, tare da ba da umurnin tsare shi a gidan kaso na garin Kollo, kafin a kammala sauran bincike da gudanar da shari'a a nan gaba.
Hajiya Houssei Manzoumbou, shugabar Kungiyar mata ‘ya'yan Sarakouna a Nijar ta nuna takaicinta kan wannan lamari tare da bayyana fatan kotu za ta yi wa kowa adalci a cikin shari'ar.
Karin bayani: Nijar: Kotun koli ta ja kunnen 'yan siyasa
Duk da cewa lamarin na a matsayin zargi a halin yanzu a gaban kotu, amma ya sake farfado da muhawara kan zargin da aka jima ana yi wa wasu malamai da shugabannin makaranta na ci da gumin dalibansu musamman mata a makarantun kasar da dama, kamar yadda Abdou Lokoko na kungiyar ROSEN da ke kare martabar ilimi a Nijar ya bayyana.
Kungiyoyi da dama sun bayyana fatan ganin kotu ta zurfafa bincike domin gano gaskiyar abin da ya wakana don kare mutunci da kuma hakkin ministan da ma dalibar a wajen zartar da hukunci.
Sai dai Abdourahmane Ide, wani dan fafutikar kare hakin dan Adam a Nijar, ya ce bai kamata ba mutane su dinga saurin yanke hukunci kan mutuman da ake zargi, wanda a ido doka ba shi da laifi matukar kotu ba ta tabbatar da zargin ba.
Karin bayani: Nijar: Ko Tchangari zai shaki iskar 'yanci?
Jama'a sun zura ido su ga yadda wannan shari'a ta zargin fyade za ta kaya, ta la'akari da yadda kotunan Nijar suka dage wajen kwatanta gaskiya a shari'o'i har masu cike da sarkakiya, inda ko a makonni biyu da suka gabata ta wanke tsaffin ministoci biyu daga zarge-zargen da aka yi masu tare da sallamarsu domin komawa cikin iyalinsu.