1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Murna da wucewar motocin dakon kaya

Salissou Boukari
February 9, 2026

Al'ummar Nijar sun yi farin ciki da yarjejeniya tsakanin hukumomin kwastam na Najeriya da na Nijar wanda ya bayar da damar ficewar daruruwan motocin dakon kaya na Nijar da suka dade a kan iyakar Benin da Najeriya

https://p.dw.com/p/58NzT
Motocin dakon kaya akan iyakar Nijar da Najeriya
Motocin dakon kaya akan iyakar Nijar da NajeriyaHoto: BOUREIMA HAMA/AFP

Kimanin motocin dakon kaya 1600 ne na Nijar suka makale tsawon watanni a kan iyakar Benin da Najeriya bayan da kayayakin suka fito daga tashar Ruwan Cotonou saboda rufe rufe iyakar Nijar da Benin. Hukumomin Kwastam ko Douane na kasashen biyu sun yi wani zaman na musamman domin magance matsalar inda shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin barin motocin su wuce.

Karin Bayani: Binciken kaya da daga Najeriya zuwa Nijar

Motocin dakon kaya a iyakar Nijar da Benin ta Malanville
Motocin dakon kaya a iyakar Nijar da Benin ta Malanville Hoto: AFP/Getty Images

Daga Nashi bangare mai bai wa ministan kula da harkokin kasuwanci da masana'antu na kasar ta Nijar shawara Nayoussa Djimraou, ya ce batun kasuwanci abu ne da ya shafi al'umomin kasashe kai tsaye saboda haka akwai bukatar kawar da rashin jittuwa don dorewar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Karin Bayani:Bambancin ra'ayi kan rashin bude wasu iyakokin Nijar

Ga masu sharhi kan harkokin siyasar kasa da kasa da tsaro irin su farfesa Dicko Abdourahamane Malamai na Jami'ar birnin Damagaram, wannan masalaha da aka samu abin jinjinawa ne ga shugabannin Najeriya da na Nijar da aka yi hakan da amincewarsu

Karin Bayani:Hare-hare kan motocin dakon kaya a Nijar

Motocin dakon kaya a iyakar Nijar da Benin ta Malanville
Motocin dakon kaya a iyakar Nijar da Benin ta Malanville Hoto: AFP/Getty Images

Abun jira agani dai shine ko wannan mataki zai dore ba tare da wani cikas ba? har ma da kasar Benin inda wasu daga cikin kayayakin yan kasuwar ta Nijar ke bi ta tashar ruwanta su ratsa Najeriya ta yankin Segbana na kasar Benin saboda rufe iyaka ta tsakanin Nijar da Benin