1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Ramaphosa ya ki murabus duk da barazanar tsige shi

May 12, 2026

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ki yin murabus duk da sabon yunkurin tsige shi daga mulki kan zargin boye kudade da rashin sanar da ‘yan sanda, lamarin da ya sake jefa siyasar kasar cikin rudani.

https://p.dw.com/p/5Desl
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril RamaphosaHoto: Willy Kurniawan/REUTERS

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewa ba zai yi murabus daga mulki ba, duk da sabon matsin lamba da kiraye-kirayen neman ya sauka daga kan karagar mulki.

Lamarin ya biyo bayan hukuncin da kotun tsarin mulkin kasar ta yanke a ranar 8 ga watan nan, inda ta ce majalisar dokokin kasar ta saba wa kundin tsarin mulki a matakin da ta dauka na dakile yunkurin tsige shugaban kasar daga mulki.

Tun da fari dai, a bana ne majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta kafa wani kwamiti mai zaman kansa domin binciken badakalar kudade da ake alakanta da Ramaphosa. Kwamitin ya gano yiwuwar shugaban kasar ya aikata ba daidai ba bayan sace wasu kudade kimanin dala dubu 580 da aka boye a gonarsa a shekarar 2020, ba tare da sanar da ‘yan sanda ba.

A ranar Litinin, majalisar dokokin kasar ta bukaci kakakinta Thoko Didiza da ta fara shirye-shiryen aiwatar da tsarin tsige shugaban kasar, bisa zargin rashin kai rahoton kudaden ga hukumomin tsaro.

Wata masaniyar harkokin siyasa Dr. Thelele ta ce hukuncin kotun bai tabbatar da cewa Ramaphosa ya aikata laifi ko akasin haka ba, sai dai ya sake bude muhawara kan bangaren shari'a da siyasa.

Afirka ta Kudu | Shugaba Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril RamaphosaHoto: Chris McGrath/Getty Images

A nasu bangare, jam'iyyun adawa sun bukaci shugaban kasar ya yi murabus, suna masu zarginsa da halasta kudaden haram ba tare da bayyana asalinsu ba. Sai dai Ramaphosa ya musanta duk zarge-zargen, tare da jaddada cewa zai kalubalanci sakamakon binciken domin tabbatar da gaskiya.

Kakakin majalisar dokokin kasar Thoko Didiza ta ce za a bi tsarin doka wajen ci gaba da shirin tsige shugaban kasar, bayan hukuncin kotun tsarin mulki kan sashe na dokokin majalisa da aka ce ya sabawa kundin tsarin mulki.

Sabon rikicin siyasar ya haifar da rudani a cikin jam'iyyar ANC mai mulki, lamarin da ya sa aka kira taron gaggawa na shugabannin jam'iyyar.