1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta dauki alhakin hadarin jirgin Azerbaijan

Abdul-raheem Hassan
October 10, 2025

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince a karon farko, kasarsa ta taka rawa a hadarin jirgin saman fasinja na Azabaijan a shekarar 2024, yana mai bayyana hakan a matsayin "abin takaici".

https://p.dw.com/p/51j35
Wladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Wladimir PutinHoto: Sergei Bobylev/TASS/picture alliance

A ganawar da ya yi da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, Putin ya ce makami mai linzamin da dakarun tsaron saman Rasha suka harba don kai wa wani jirgin saman Ukraine mara matuki ya fashe ne a kusa da filin jirgin saman Azerbaijan da ke da ke Baku maimakon Grozny, babban birnin yankin Jamhuriyar Chechnya ta Rasha a ranar 25 ga Disambar shekara ta 2024.

Putin ya ce Rasha ta aike da makamai masu linzami, domin lalata jiragen yakin Ukraine mara matuka a ranar da lamarin ya faru, inda ya ce sun fashe ne a 'yan mitoci kadan da jirgin.

Putin ya jadda da cewa zai yi duk abin da ya dace musamman bangaren biyan diyya, kuma za a yi la'akari da daukar mataki kan jami'an da ke da hannu a harin.

Hukumomin Azabaijan sun tabbatar da mutuwar mutane 38 cikin fasinjoji 67 da suka shiga jirgin da ya fado a yammacin Kazakhstan.

Kwanaki bayan hadarin, Putin ya nemi afuwar Aliyev game da abin da ya kira "mummunan lamari" amma ya kasa amincewa da alhakin harin. Aliyev, a halin da ake ciki, ya soki Moscow saboda kokarin "yin shiru" kan abin da ya ke ganin laifinta ne.

Takaddamar da aka samu kan hatsarin jirgin ya haifar da dagulewar alaka tsakanin Moscow da Baku a baya. Dangantakar su ta kara tsami ne sakamakon mutuwar 'yan kabilar Azabaijan da 'yan sanda suka yi wa kawanya a wani birnin Rasha a watan Yuni da kuma jerin kame 'yan kasar Rasha a Azerbaijan.