'Rasha za ta mayar da martani mai zafi idan aka farmata'
September 27, 2025
Babban jami'in diflomasiyar Rasha ya yi gargadin cewa kasarsa za ta mayar da martani mai zafi ga duk wani nau'in hari da aka kai mata.
Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ne bayyana hakan da yammacin Asabar yayin da ya ke yi wa zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya jawabi a birnin New York na Amurka.
Berlin na zargin Moscow da yi wa nahiyar Turai barazana
Kalaman nasa sun biyo bayan shugaban Amurka Donald Trump ya mara wa NATO ne baya kan batun da ta yi na harbo jiragen Rasha da za su keta sararin samaniyar NATO.
Lavrov ya ce Rasha ba ta da niyyar kaddamar da hari kan NATO, amma duk wani hari da za a kai mata za ta mayar da martani.
NATO ta gargadi Rasha kan keta sararin samaniyar mambobinta
A ranar Talata aka tambayi Trump ko yana ganin ya dace kasashen NATO su harbo duk wani jirgin Rasha da zai bi ta sararin samaniyarsu, sai ya ce eh yana ganin haka ne.