1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rawar da rundunar sojin Turai za ta taka

Abdullahi Tanko Bala
December 16, 2025

Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius ya ce matakin da rundunar sojin Tarayyar Turai za ta taka wajen bayar da kariya ga Ukraine ya dogara da halayyar shugaban Rasha Vladimir Putin

https://p.dw.com/p/55U2F
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius
Ministan tsaron Jamus Boris PistoriusHoto: Christoph Soeder/dpa/picture alliance

Kalaman ministan na zuwa ne kwana guda bayan da shugabanin Tarayyar Turai suka gana a Berlin inda suka yanke shawarar kafa rundunar tsaro ta musamman domin taimakawa wajen cimma tsagaita wuta a Ukraine.

A baya dai Rasha ta yi watsi da shirin tura sojojin kasashen ketare domin sa ido kan tsagaita wuta.

Wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin turan suka fitar ta ce rundunar sojin ta tarayyar Turai na jaddada goyon baya ga shirin Amurka na bayar da kariya ga UKraine tare da kare sararin samaniyarta idan ma hali ya kama suojojin Turan na iya shiga cikin Ukraine don taimakawa.