Rubio: " Kungiyar NATO ta ki yi komai" game da yakin Iran
May 21, 2026
Jim kadan kafin tashinsa zuwa Sweden inda zai halarci taro da takwarorinsa na NATO, Rubio ya shaida wa manema labarai cewar Shugaba Donald Trump "ba ya rokonsu su ba da gudunmawar sojoji ko aika jiragen yaki, amma duk haka sun ki yin komai game da wannan batu." lamarin da a cewarsa yake bata masu rai.
Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-hare a Iran a ranar 28 ga Fabrairu ba tare da Donald Trump ya tuntubi mambobin NATO ba, sannan manyan kawayensu na Turai sun nuna shakku kan amfanin yakin da ya sa farashin mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi.
Sai dai sakataren harkokin wajen Amurka ya ce "kasashe da yawa na kungiyar NATO na da ra'ayin cewar ka da a bar Iran ta mallaki makaman nukiliya domin barazana ce ga duniya, yana mai jaddada cewa Shugaba Trump ya yunkura ne domin tabbatar da wnanan tunani.
Ministocin harkokin wajen NATO suna taro ne a yau Alhamis da gpobe Juma'a a Helsingborg da ke kudancin Sweden don tattaunawa kan goyon bayan Ukraine da kuma shirya taron kungiyar na gaba a Turkiyya a watan Yuli.