1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ADC ta nuna shakku kan zabukan 2027

Uwais Abubakar Idris ZMA
April 2, 2026

Jam'iyyar adawa ta ADC ta ayyana yanke kaunar INEC za ta yi mata adalci 2027, tare da bukatar sauke shugaban hukumar.

https://p.dw.com/p/5Bbu6
Hoto: Nasiru Salisu Zango

Jam'iyyar ta mayar da martani ne a kan  matakin da hukumar zabe ta dauka na cire sunayen shugabaninta a matsayin wadanda take hulda da su.

Kusan daukacin jiga-jigan ‘yan adawa ba kawai na jamiyyar ADC ba har ma da wasu jam'iyyu ne suka hallara a wajen taron ‘yan jarida da aka gudanar a Abuja. Sun bayyana fushinsu da matakin da hukumar zaben ta Najeriya ta dauka a kan jam'iyyar adawa ta ADC wacce suka ce ita ce madafa ta karshe ga ‘yan kasar. Sanata David Mark shi ne shugaban jamiyyar wandaya fara jawabi a kan hatsarin da ke fusknatar kasar.

‘'Bukatarmu mai sauki ce, ko dai shugaban hukumar zabe ta Najeriya ya sauka daga mukaminsa, ko kuma a kore shi daga aiki. Ba mu da tabbacin za su iya gudanar da sahihin zabe. Wannan hukumar zaben karkashin Farfesa Josiah Amupetan duk abinda ya faru sune ke da laifi sakamakon wannan matakin da suka dauka''.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma jigo a jam'iyyar ADC Atiku Abubakar na cikin wadanda suka bayyana fahimtarsu a kan matakin da hukumar zaben Najeriyar ta dauka a kan jam'iyyar tasu da suka ce manufa ce ta murkushe ‘yan adawa.

Rigingimun dai na ta afka wa jam'iyyun adawar Najeriyar kama daga PDP da ta Labour yanzu kuma ga ta ADC tana neman bin sahu,  duka a dalili na rigigimu na cikin gida.

A yanzu jam'iyyar ADC ta yanke hukuncin cewa duk da wannan mataki da hukumar zaben ta dauka za ta ci gaba da babban taronta da ta shirya domin ta sanar da hukumar zabe tun kafin daukan wannan mataki. Irin mutanen da suka hallara ya nuna yadda wannan lamari ya sanya harkar siyasar Najeriyar ya dau dumi a kan wannan lamarin.