SiyasaAfirka
Rukunin farko na 'yan Najeriya sun dawo daga Afirka ta Kudu
June 11, 2026
Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce jirgin da ya sauka a birnin Lagos ya dauko fasinjoji 262 tare da jami'ai uku.
Tun daga watan Afrilu, an shafe makonni ana gudanar da zanga-zangar kin jinin bakin haure a sassan Afirka ta Kudu, lamarin da ya kara haifar da takaddama tsakanin 'yan kasar da ma'aikata 'yan kasashen waje.
Wasu 'yan kasar ta Afirka ta Kudu na zargin bakin haure da kwace musu guraben aiki, yayin da hukumomin kasar suka yi Allah wadai da zanga-zangar, suna mai bayyana ta a matsayin nuna kyamar baki.
Ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta ce shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin kwaso 'yan Najeriya da ke ganin rayuwarsu na cikin hadari sakamakon ci-gaba da zama a Afirka ta Kudu.