Sabuwar takaddama tsakanin Hungary da Ukraine
February 25, 2026
Matakin na Orban ya biyo bayan zargin da Hungary da kuma Slovakia ke yi wa Ukraine kan katsewar bututun man fetur na Druzhba, wanda ya ratsa Ukraine dauke da danyen man Rasha zuwa kasashen biyu.
Sai dai Kyiv, wadda har yanzu ba ta mayar da martani kan sabbin zarge zargen ba, ta ce hare haren jiragen yaki marasa matuka na Rasha ne suka lalata bututun, kuma ana kan aikin gyarawa.
A nata bangaren, kungiyar tarayyar turai ta tabbatar da cewa babu wata barazanar karancin man fetur nan kusa ga Hungary ko Slovakia, domin su na da wasu hanyoyin samar da mai.
Orban, wanda ya dakatar da amincewar ba da bashin euro biliyan 90 da Tarayyar Turai ke shirin bai wa Ukraine, da kuma sabbin takunkumi kan Rasha, har sai an bude bututun, ya ce an rufe bututun ne saboda dalilai na siyasa, ba na fasaha ba.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Orban ya ce ya samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar karin matsala ga tsarin makamashin kasarsa.