1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin mutane na cikin barazanar yunwa a Afirka

Zainab Mohammed Abubakar
January 16, 2026

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 55 da rikicin yankunan yammaci da tsakiyar Afirka ya daidaita, suna fuskantar matsalar karancin abinci.

https://p.dw.com/p/56yQK
Hoto: DW

Rahotanni na nuni da cewa mutane na gab da fuskantar matsanancin yunwa a arewacin Najeriya.

Hukumar tallafin abinci ta MDD ta ce, tashin hankali a yankin ya haifar da matsalar yunwa, daura da rage tallafin abinci da ya kara ta'azzara lamarin, inda rage abincin ya zama wajibi yayin da kudade ke karewa.

Darektan nazarin abinci mai gina jiki da samar da shi na hukumar Jean-Martin Bauer ya fadawa manema labarai a Geneva cewar, a yammaci da tsakiyar Afirka mutane miliyan 55 za su fuskanci matsalar karancin abinci a lokacin bazara, tsakanin watan Yuni da Agusta na wannan shekara ta 2026.