LafiyaNa duniya
Sauye-sauye a hukumar lafiya ta duniya
February 2, 2026
Talla
Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya bayyana a wannan Litinin cewa kudin hukumar da aka zabtare sakamakon shirye-shiryen ficewar Amurka, haka ya haifar da wata dama ta sake fasalin hukumar.
Tasirin matakin
Bisa al'ada Amurka ke kan gaba wajen bayar da kudin tafiyar da hukumar kafin daga bisani gwamnatin Shugaba Donald Trump ta janye daga hukumar baki daya.
A wajen taron hukumar ta Lafiya ta duniya na shekara-shekara shugaban, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya shaida wa manyan jami'an hukumar cewa janyewar Amurka ya haifar da gibi kuma lokaci mai tsauri a tarihin hukumar, amma ana iya amfani da yanayin da ake ciki wajen kawo sauye-sauye na rage ma'aikata da fayyace abubuwan da za a bai wa muhimmanci.