1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Ko za a samu sauyi a INEC?

Uwais Abubakar Idris LMJ
October 8, 2025

Wa'adin shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC mai barin gado Farfesa Mahmood Yakubu ya kawo karshe, kuma ana samun ra'ayoyi mabanbamta kan yadda ta tafiyar da hukumar.

https://p.dw.com/p/51fgr
Najeriya | Hukumar Zabe | INEC | Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban Hukumar Zaben Najeriya INEC mai barin gado Farfesa Mahmood YakubuHoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto/picture alliance

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya mai Zaman Kanta ta Kasa INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya kammala wa'adin mulkinsa, a yayin da aka fara waiwayen irin abubuwan da suka faru a lokacin da yake jagorancin hukumar a kokarin kyautata yanayin zaben kasar da ke cike da takaddama. 

Kawo karshen wa'adin aikina shugaban hukumar ta INEC a Najeriya dai babban al'amari ne, musamman ga Farfesa Yakubu da ya kwashe tsawon shekaru 10 yana jagorantar hukumar. An dai ga sauye-sauye na bullo da amfani da kimiyya da fasaha a zaben, a kokarin zamanantar da aikin hukumar ta INEC ya dace da matakin kasa-da kasa.

Akwai tarin kalubale

Sai dai ya fuskanci kalubale iri dabam-dabam ba, har ma sai da aka dage zaben shugaban kasar a shekara ta 2019 a karkashin jagorancinsa. Shugaban hukumar zaben Najeriyar mai barin gado shi ne yafi dadewa a kan wannan mukami a tarihin hukumar ta INEC, saboda yadda zama cike da santsi da kan kai wadanda suka rike mukammin har kasa.

Karin Byani: Dalilan dage zaben Najeriya

Duk da wadannan ci-gaban da ake ganin ya samu musamman amfani da kimiyya da fasaha a zaben Najeriyar, ana diga ayar tambaya a kan yadda ya gudanar da zaben 2023 da aka sa ran samun ci-gaba sosai saboda amfani da kimiyya da fasaha wajen tattara sakamakon zaben da aika shi ta kafar Internet.

Nasarori ko akasin haka?

Ko waye zai lashe zaben Najeriya na 2023

A yayin da ake shirin kafa sabuwar tafiya a hukumar zaben Najeriyar da ke fuskantar zabubbuka masu zuwa, nasarori da takaddamar da ta biyo wa'adin mulkin shugaban hukumar ta INEC ya sanya 'yan siyasa da mafi yawansu ke bangaren adawa ganin ya bata rawarsa da tsalle. A ganinsu akwai bukatar idan ya natsu, ya warware zare da abawar abin da ya faru.

A yanzu dai kallo ya koma sama a kan wanda za a nada da zai jagoranci gagarumin aiki na hukumar da ke da tasiri sosai musamman sauye-sauyen da majalisa ke shirin yi ga dokokin zaben kasar, abin da zai nuna makomar dimukuradiyyar Najeriyar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani