WasanniAfirka
Senegal da Mali sun kai wasan dab da na kusa da na karshe
January 4, 2026
Talla
A gasar cin kofin nahiyar Afirka da ke wakana yanzu haka a kasar Morocco, Senegal ta samu damar shiga zagayen dab da na kusa da na karshe, bayan casa Sudan 3-1 da yammcin Asabar.
Haka zalika Mali ta samu zuwa wannan mataki, bayan doke Tunisia 3-2 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, biyo bayan tashi 1-1 a mintuna 120.
A wannan Lahadi mai masaukin baki Morocco za ta fafata da Tanzania, da karfe 5 na yamma agogon Najeriya da Nijar.
Sai karawa tsakanin Afirka ta Kudu da Kamaru, da karfe 8 na dare.
A ranar Litinin Najeriya za ta yi wasanta da Mozambique, da karfe 8 na dare.