Senegal na shirin aiwatar da manufofinta
November 19, 2024
Talla
Tun farko gwamnatin Diomaye Faye ta fuskanci cikas wajen aiwatar da kasafin kudi tun bayan zaben shugaban kasar saboda rashin rinjaye a majalisar. Daga cikin abin da gwamnatin za ta sake dubawa har da batun sake yarjejeniya cinikayya da kasashen ketare kan ma'adinai da sauransu. A hasahen da kafofin yada labarai dabam-dabam suka yi kan sakamakon wucin gadi na zaben, jam'iyyar ta Pastef na da kusan kashi uku cikin hudu na kujerun majalisar 165.