1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta bukaci a ninka hukuncin aikata auren jinsi

February 24, 2026

Firaministan Senegal, Ousmane Sonko, ya gabatar da wani kudirin doka da ke neman a ninka hukuncin daurin kurkuku kan masu auren jinsi.

https://p.dw.com/p/59Lgv
Firaministan Senegal Ousmane Sonko
Firaministan Senegal Ousmane SonkoHoto: Seyllou/AFP

Da yake jawabi a majalisar dokokin kasar a wannan Talata, Sonko ya ce duk wanda aka samu da aikata auren jinsi zai fuskanci daurin shekaru biyar zuwa goma, maimakon shekara daya zuwa biyar kamar yadda doka ta tanada a yanzu.

Kudirin, wanda har yanzu yana jiran kada kuri'a a majalisa, zai gyara kundin dokokin hukunta laifuka na Senegal domin fayyace cewa duk wata hulda ta jima'i tsakanin jinsi guda laifi ne.

Matakin na zuwa ne bayan kama wasu mutane ciki har da fitattun jama'a, yayin da kungiyoyin addini ke matsa lamba a kara tsaurara hukunci kan masu jima'i da jinsinsu.