Senegal ta fara tsuke bakin aljihu saboda yakin Iran
April 4, 2026
Senegal kamar wasu kasashen Afirka da dama, na shigar da man fetur din da suke amfani da shi ne daga ketare, inda a yanzu rufe mashigin Hormuz ke tasiri sosai, wanda ke haifar da tsadar kaya a kasuwanni.
Karin bayani: Tsadar rayuwa a Senegal shekara guda cikin mulkin Faye
Firanminstan kasar Ousmane Sonko ya ce, gwamnatinsa a yanzu na daukar matakan rage kashe kudi, yana mai nuni da cewa kwarya-kwaryar kasafin kudin kasar na farko ya dogara ne kan farashin mai na dalar 62 kan kowacce ganga, wanda a yanzu ya ninka sau biyu sakamakon yakin Iran.
Ya kara da cewa ya soke tafiye-tafiye da dama da ya shirya yi, ciki har na ziyarar ayyuka da zai kai kasashen Nijar da Spain da kuma Faransa. A cewarsa, babu wani minista da zai yi tafiya zuwa ketare ba tare da wani babban dalili ba.