Senegal ta karyata sake cin bashi a asirce
March 25, 2026
Hukumomin gwamnatin Senegal sun kare matsayarsu da cewa bai saba da ka'idojin kasuwanci ba. Gwamnatin, wacce ta karbi mulki a watan Afrilun 2024, ta zargi tsohuwar gwamnatin Macky Sall da boye bayanai a kan dimbin basussukan da ake bin kasar.
Jaridar Financial Times wacce ake bugawa a Birtaniya, ta ruwaito cewa sabuwar gwamnatin Dakar ta "karbo Yuro miliyan 650 daga masu ba da lamuni na ci gaban Africa Finance Corporation da kuma babban bankin Abu Dhabi a 2025 a matsayin karin bashin da ke kan kasar."
A farkon watan Maris, Senegal ta biyan bashin dala miliyan 471, duk da fargabar da masana tattalin arzikin kasar ke yi kan gibin kasafin kudi na kusan kashi 14 cikin 100 GDP da basussukan ma'aikatun gwamnati da aka kiyasta kashi 132 cikin 100 na abin da kasa ke fitarwa a karshen shekarar 2024.