A kwanakin nan siyasar Najeriya ta sake daukar wani sabon salo bayan da gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya fice daga PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki.
Matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan siyasa da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum.
Shin don wa 'yan siyasar Najeriya ke komawa jam'iyyar APC?