Ina makomar adawa a Najeriya?
November 18, 2025
An dai kai har ga harba hayaki mai saka kwalla da nufin hana wani rikici a tsakanin bangarorin da ke gwagwarmaya ta neman iko na mallakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP da duk ke taro cikin gidan na Wadata.
APC tana mamaya
Ya zuwa yanzun dai APC yar mulkin na kara nuna alamun cikar kwari, kuma kama dag Kogi zuwa ga Bayelsa ko bayan Enugu da Delta da ma Akwa Ibom dai sannu a hankali jam'iyyar na hadiye 'yan adawa.
Gwamnoni kusan biyar ko bayan 'yan majalisun dattawa da na tarayya suka fice zuwa cikin APC a wani abun da ke nuna alamun hadiya a bangare na masu tsintsiyar. To sai dai kuma murna a tsakani na masu tsintsiyar na neman ta tsaya a wuya sakamakon tsoron da ke ta kara bayyana a rassa na jihohi.
APC ba ta tsira ba
Duk da cewar dai a zauren taro ana ta murmushi, can a cikin kuryar daki dai, ana kallon karuwar cacar baka tsakanin tsofaffi na masu tsintsiyar da sababbin da ke tururuwar a halin yanzu.
Can a jihar Taraba in da gwamnan jihar yake shirin barin PDP domin komawa ya zuwa APC, rikicin na neman rikidewa ya zuwa sigar addini.
A yayin kuma da a Pleatau ake ta jan kafa da adawar komawargwamnan cikin gidan na masu tsintsiya bisa tsoron kwace ragamar harkokin jam'iyyar.
A shekara ta 2014 dai PDP da ke cikin babban rikici dai tai cikar kwari kafin wani rikicin cikin gida bisa buri ya kai ga hujewar da masu lemar ke take kokarin dinkewa har ya zuwa yanzu.
Makomar PDP
Can cikin gidan PDP ma dai sai da ta kai ga harba bindiga sakamakon rikicin da ya mamaye gidan na Wadata in da bangarorin biyu ke fafutukar neman tabbatar da karfin iko yanzu haka.
An dai jibge jami'an tsaro a hedikwatar jam'iyyar da nufin hana rikici a tsakanin bangaren Nysom Wike da ya fara isa cikin gidan na Wadata ya nemi hana sabbabi na shugabannin na Ibadan damar isa cikin gidan.
An dai gwabza da ma musaya ta hayaki mai sa kwalla kafin bangaren na Kabiru Turaki ya samu damar kai wa cikin gidan.
Najeriya dai tana tsakanin tabbatar da dorewar demukaradiyya mai inganci da kila kama karyar da ke da tasiri ga rayuwa da makomar miliyoyi cikin kasar.