1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin samar da zaman lafiya a Gaza na samun martani

Mahmud Yaya Azare M. Ahiwa
September 30, 2025

Ana samun martani mabambanta dangane da shirin da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar don kawo karshen yaki a Gaza. A yayin da wasu ke maraba da shi wasu kuwa suna ci gaba da yin taka tsantsan ne da shirin.

https://p.dw.com/p/51Hku
USA Washington D.C. 2025 | Benjamin Netanjahu und Donald Trump bei gemeinsamer Pressekonferenz
Hoto: Win McNamee/Getty Images

Shirin da shugaban na Amurka Donald Trump ya gabatar a yayin ganawarsa da 'yan jarida tare da firaministan Isra'ila Banjemin Netanyahu da ya ziyarci shugaban na Amurka, an yi masa lakabi ne da Peace Plan, wato shirin zaman lafiya, wanda shugaban Trump din ya ce zai samar da zaman lafiya mai dorewa ne ba a zirin Gaza da Isra'ila kadai ba, har ma a daukakacin yankin Gabas Ta Tsakiya:

"Yau wata rana ce da ta shiga tarihi kan batun samar da zaman lafiya ba a Zirin Gaza da Isra'ila kadai ba, har a yankin Gabas Ta Tsakiya. Zaman lafiyar da zai share fagen bunkasa tattalin arziki da zumunci tsakanin kasashen yankin baki daya, cikin su har da kasar Iran a karkashin yarjejeniyar dunkulewar zuriyar Annabi Ibrahima. Irin goyan bayan da wannan shirin ya samu daga kasashen yankin bai masaltuwa.”

A nasa bangaren firaministan Isra'ila Banjemin Netanyahu ya bayyana dalilansa na yin lalale maraba da wannan shirin.

"Ina goyon bayan wannan shirin naka na kawo karshen yaki a Gaza saboda zai biya bukatun Isra'ila da suka sanya ta kaddamar da yaki a Gaza. Wato dawo da wadanda ake tsare da su da raba Hamas da mulkin Gaza, gami da samun tabbacin zirin ba zai sake zama barazana ga tsaron Isra'ila.”

Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Shugaba Trump na Amurka
Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Shugaba Trump na AmurkaHoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Shi dai wannan shirin na dauke da sakin layi 20 ne da ke fayyace matakan samar da zaman lafiya a zirin na Gaza, kama tun daga kawo karshen yaki da ficewar dakarun Isra'ila daga daukakain Zirin Gaza, gami da sakin illahirin wadanda Hamas ke garkuwa dasu,das akin daruruwan firsinonin Falalsdinawa, har zuwa ga sake gina zirin nda tafiyar da ikonsa karkashin gwamnatin gamin gambiza ta kwararun Falalsdinawa da na kasashen ketare, karkashin jagorancin shi kansa shugaban na Amurka da zai zama shugaban kasar wucin gadi na zirin na Gaza, a yayin da tsohon firaministan Burtaniya Tony Blair zai zamo firaministan gwamnatin rikon kwaryar da za ta share fagen kafa ingantaccen tafarkin dimukuradiyya a zirin, kamar yadda daftarin shirin da shugaban na Amurka ya dankawa 'yan jarida ke fayyacewa.

Tuni dai shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya yaba wa shirin:

"Wannan shirin zai lalata mungun tanadin Isra'ila na mamaye Gaza da zagon kasan da Natenyahu yake yi na hana kafuwar kasar Falalsdinu.”

A yayin da ake jiran martanin kungiyar Hamas kan shirin da ta ce tana masa karatun ta nutsu, ita kuwa kungiyar Islamic Jihad cewa ta yi, shirin ba cinya ba kafar baya ake son yi wa Falalsdinawa, ta hanyar maye gurbin mamayar Isra'ila da mamayar Amurka a zirin na Gaza.

Tarayyar Turai dai ta ce shirin wata sabuwar dama ce da ya zama wajibi dukkanin bangarorin su aiwatar da shi. A yayin da kasashen Faransa da Burtaniya dai sun ce suna fatan Natenyahu zai aiwatar da shirin ba tare da kumbiya-kumbiya ba.