Shugaba Trump ya ce akwai yiwuwar tattaunawar sulhu da Iran
April 14, 2026
Jami'an diflomsiyya na aiki ta karkashin kasa, domin sake shirya zaman tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran, domin samar da yarjejeniyar dakatar da yakin Gabas ta Tsakiya baki-daya.
Wannan na zuwa biyo bayan matakin Washington na toshe mashigin Hormuz, yayin da Tehran ke barazanar far wa duk wani jirgin da ya ratsa ba bisa sahalewarta ba.
Karin bayani: Amurka ta fara killace mashigin Hormuz
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya bayyana kyakkyawan fatansa na ganin an cimma daidaido a kai, bayan da ya samu ganawa da mataimakin firaministan Pakistan, kuma ministan harkokin wajenta Ishaq Dar, inda suka tattauna batun sake bude wata sabuwar tattaunawa kan batun.
A na sa bangaren, yayin tattaunawa da jaridar New York Post, shugaba Donald Trump na Amurka, ya ce akwai yiwuwar sake zaman tattaunawar sulhun, nan da kwanaki biyu masu zuwa, a birnin Islamabad na Pakistan.
Karin bayani: Iran za ta afka wa jiragen yakin da suka doshi Hormuz
A gefe guda kuma fafatawa ta kazance a wannan Talata, tsakanin dakarun sojin Isra'ila da dakarun kungiyar Hezbollah ta Lebanon, bayan da bangarorin biyu suka yi musayar wuta a garin Bint Jbeil na kudancin Lebanon.
Wannan na wakana ne a daidai lokacin da wakilan Isra'ila da na Lebanon, ke shirin ganawa da juna a birnin Washington, bisa jagorancin sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio.
Karin bayani: Isra'ila ta ce za ta yi tattaunawar sulhu da Lebanon
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce fatansa shi ne kwance damarar kungiyar Hezbollah, domin samar da dawwamammen zaman lafiya mai dorewa.
Yayin da shugaban Lebanon Joseph Aoun, ke fatan tattaunawar sulhun birnin Washington ta haifar da yarjejeniyar tsagaita wutar yakin.