1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Shugaba Trump ya ce Iran ta kagu ta cimma sulhu da Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 7, 2026

Mr Trump ya ce a farkon mako mai kama za su ci gaba da tattaunawa da Iran kan batun kwance damararta ta kera nukiliya.

https://p.dw.com/p/58Go8
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da tawagarsa, bayan samun tarba daga takwaransa na Oman a birnin Muskat
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da tawagarsa, bayan samun tarba daga takwaransa na Oman a birnin MuskatHoto: Iran Foreign Ministry/AP Photo/picture alliance

Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce a farkon mako mai kama ne za su ci gaba da tattaunawa da Iran, kan batun kwance damararta ta kera makamin nukiliya da ma sauran batutuwan tsaro, bayan kammala zaman farko ranar Juma'a a kasar Oman.

Mr Trump wanda ya bayyana hakan ga 'yan jarida a birnin Washington, gabanin hawa jirginsa na Air Force One, a kan hanyarsa ta zuwa gidan shakatawarsa na Mar-a-Lago da ke jihar Florida, ya tabbatar da cewa hakika ganawar wakilansa da tawagar Iran ta ba da haske sosai, sakamakon yadda Iran ta nuna kaguwa da ganin an cimma masalaha.

Karin bayani : Amurka na matsa wa Iran lamba kan shirin nukiliya

A jawabin da ya yi wa gidan talabijin na Iran, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi, ya ce sun samu fa'ida a cikin wannan tattaunawa, sakamakon shiga da kafar dama, to sai dai babu wani karin bayani da ya yi kan batun ci gaba da ganawar.