1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban gwamnatin Jamus zai ziyarci Norway kan batun tsaro

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 12, 2026

Shugaba Merz da firaministan Norway da kuma na Canada za su duba atisayen dakarun tsaron NATO sama da 30,000.

https://p.dw.com/p/5ADSD
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz tare da firaministan Norway Jonas Gahr Støre yayin taro a Berlin 21.07.2025
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz tare da firaministan Norway Jonas Gahr Støre yayin taro a Berlin 21.07.2025Hoto: Uwe Koch/IMAGO

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya kama hanyar kai ziyara Norway, domin ganawa da firministan kasar Jonas Gahr Støre da yammacin wannan rana ta Alhamis.

A ranar Juma'a kuma shugabannin biyu za su kai ziyara tashar ruwan Andøya Space Port da ke yankin Andenes na kasar, cibiyar harba roka zuwa sararin samaniya, wadda ke aiki tun shekarar 1962.

Karin bayani - Jamus ta koka kan rashin sanin makomar Iran bayan yaki

Daga nan kuma za su je sansanin soji na Bardufoss, inda za su hadu da firaministan Canada Mark Carney, domin duba atisayen dakarun kawancen tsaron NATO sama da 30,000 daga kasashe 14, inda Jamus ke da dakaru 1,600 a ciki.

Ganawar jagororin za ta mayar da hankali kan batutuwan tsaro da samar da makamai da kuma hadin kan juna.