1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Siriya: Faretin sojoji don murnar shekara da kifar da Assad

Mouhamadou Awal Balarabe
December 8, 2025

Dubban 'yan Siriya sun gudanar da gangami da fareti a titunan Damascus domin murnar zagayowar ranar da gwamnatin Bashar al-Assad ta fadi, yayin da shugaban kasa Ahmed al-Sharaa, ya yi kira ga hadin kai.

https://p.dw.com/p/54x9M
Sojoji da 'yan Siriya sun gudanar da biki don nuna farin cikin rabuwa da mulkin al-Assad
Sojoji da 'yan Siriya sun gudanar da biki don nuna farin cikin rabuwa da mulkin al-AssadHoto: Chris McGrath/Getty Images

Shekara guda bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad, shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya bukaci 'yan kasarsa da su hada kawunansu wuri guda don karfafa zaman lafiya da sake gina kasarsu da yakin basasa ya daidaita.

Bayan sallar asuba a Masallacin Umayyad, al-Sharaa da ke sanye da kakin soja, ya yaba da sadaukarwa da jarumtakar mayakan da suka hambarar da tsohon shugaban kasa al-Assad shekara guda da ta gabata.

Karin bayani: Al-Sharaa: Daga makiyi zuwa babban aboki?

Dubban 'yan Siriya sun gudanar da gangami a titunan Damascus domin murnar zagayowar ranar da gwamnatin Bashar al-Assad ta fadi, yayin da a daya hannun kuma Ahmed al-Sharaa, tsohon mai gagwarmayar addini ya zama shugaban kasa na wucin gadi bayan shekaru 14 na yakin basasa da kuma fiye da shekaru 50 na mulkin danniya na iyalan al-assad.

Sai dai tashin hankalin da ya yi sanadiyyar zubar da jini a tsakanin tsiraru na al'umomin Druze da Alawite, da kuma ayyukan soji na Isra'ila da ke makwabta da Siriya sun kawo rauni ga sauyin da aka samu.

Karin bayani: Al-Sharaa: Mai kaifin kishin addini ko dan gata?

kasar Syria ta koma cikin dangi inda aka dage mata takunkumin kasa da kasa bayan hambarar da gwamnatin al-Assa, amma har yanzu kasar na fuskantar manyan kalubale na tsaro.