Sojoji da 'yan ta'adda sun kashe mutane kusan 2000 a Burkina
April 2, 2026
Wani rahoto da hukumar kare hakkin 'dan adam ta duniya Human Rights Watch ta fitar, ya nuna cewa kimanin fararen hula 1,837 aka kashe a kasar Burkina Faso, daga Janairun 2023 zuwa Agustan 2025, sanadiyyar ayyukan sojojin kasar da kuma 'yan ta'adda.
Wannan kuma daidai yake da aikata laifukan yaki, in ji Human Rights Watch, wadda ta ce sojojin kasar suna aikin hadin gwiwa ne da dakarun sa kai da aka dauka, domin agazawa jami'an tsaro wajen yakar 'yan ta'adda, amma suke fake da hakan suke cin karensu babu babbaka.
Karin bayani: EU na shirin sake samun karfin fada a ji a yammacin Afirka
Human Rights Watch ta tattara wadannan alkaluma ta hanyar bibyar jama'a da daukar hotuna da bidiyo, a kasashen Burkina Faso da Jamhuriyar Benin da Côte d'Ivoire, sai Mali da kuma Ghana.
Karin bayani: Ghana da Burkina Faso sun kulla yarjejeniyar tsaro
Tun bayan kwatar mulkin Burkina Faso da tsinin bindiga a Satumban 2022, Kyaftin Ibrahim Traore, ya gaza magance matsalolin tsaro da kungiyoyi masu ikirarin jihadi ke haddasawa a kasar, wadanda suka hada da JNIM mai alaka da Al-Qaeda sai kuma IS.