1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya ta yi martani kan matsayar Isra'ila kan Somaliland

December 28, 2025

Gwamnatin Somaliya ta nuna rashin jin dadi da matakin da Isra'ila ta dauka na amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa kamar kowacce a duniya. Wannan martani ya fito ne a wannan Lahadi daga Somaliyar.

https://p.dw.com/p/5637m
Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud
Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh MohamudHoto: Odd Andersen/AFP/Getty Images

Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud, ya bayyana cewa matakin Isra'ila na amincewa da yankin Somaliland a matsayin kasa mai ‘yanci, babbar barazana ce ga tsaro da zaman lafiya a duniya, kuma yana shafar lamirin kasa da muradin al‘uma.

A taron gaggawa na Majalisar Dokoki da aka yi a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, Sheikh Mahamud ya ce wannan mataki daidai yake da hari ga iko da ‘yanci da hadin kan kasar Somaliya.

Yankin Somaliland dai ya bayyana ballewa daga Somaliya ne a shekarar 1991.

Duk da gudanar da harkokinta na gwamnati da samar da kudinta da ma sojoji, har yanzu ba ta samu amincewar kasashen duniya.

Wannan mataki na Isra'ila na iya haifar da rudani, kamar yadda shugaban na Somaliya ke kiran da a kiyaye diyaucin kasar da ma muradin al'uma.