1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Starmer da Trump za su tattauna batutuwan duniya

Suleiman Babayo AMA
September 18, 2025

Shugaban Amurka da firaministan Birtaniya suna ci gaba da tattauna batutuwa yayin da shugaban na Amurka ke ci gaba da ziyarar aiki a Birtaniya kuma ana sa ran saka hannu kan kudirori da dama tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/50eYZ
Shugaba Donald Trump na Amurka da Sarki Charles na III
Shugaba Donald Trump na Amurka da Sarki Charles na IIIHoto: Evan Vucci/AP Photo/dpa/picture alliance

A wannan Alhamis Shugaba Donald Trump na Amurka wanda yake ziyarar aiki a kasar Birtaniya zai tattauna batutuwan da suka shafi kasashen duniya tare da Firaminista Keir Starmer.

Muhimamncin ziyarar

Shugaba Donald Trump na Amurka da Sarki Charles na III
Shugaba Donald Trump na Amurka da Sarki Charles na IIIHoto: Kirsty Wigglesworth/AFP

Lokacin ziyarar shugaban na Amurka ya gana da manyan jami'an Biraniya da suka hada da Sarki Charles na uku. Kasashen sun tattauna farfafa harkokin kasuwanci da juna jari tsakanin su.

Ana kuma sa ran kasashen biyu da suka dade suna hulda ta musamman za su saka hannu kan kudirori da dama na fasaha da makamasi gami da kimiyya.