Sudan: An kashe gomman mutane a asibiti
March 22, 2026
Talla
Babban daractan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce harin ya rutsa da yara 13 da ma'aikatan jinya da kuma marasa lafiya da dama. A sakon da ya wallafa a sahfinsa na X, Tedros ya ce harin na asibitin koyarwa na Al Deain ya haifar da daina aiki a asibitin.
Karin bayani: Shin ana iya kawo karshen rikicin Sudan?
Ya kuma ce wasu mutum 89 sun jikkata a harin da ake zargin rundunar sojin kasar ce ta kai da jirgi mara matuki. Alkalumman WHO sun yi nuni da cewa, fiye da mutane 2,000 ne aka kashe a hare-hare fiye da 200 kan asibitoci tun bayan fara yakin basasa a Sudan a shekarar 2023.