Sudan: Kuncin rayuwa ta yi tsanani
December 20, 2025
Ziyarar na zuwa ne yayin da fadan da ya barke tsakanin sojojin Sudan da mayakan sa kai na RSF a watan Afrilun 2023 ya ke kara yin kamari a kudancin Kordofan, lamarin da ke kara tayar da hankali na aukuwar ta'asa makamancin wanda ya faru a birnin El-Fasher a karshen watan Oktoba.
An ruwaito karuwar kashe kashe da fyade da sace mutane tun bayan da RSF ta kame yammacin Darfur.
Babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce a shirye yake ya yi aiki da Trump domin kawo karshen rikicin bayan tattaunawa da yarima Mohammed Bin Salman.
Kasar Saudiyya na daga cikin kasashe hudu da ke shiga tsakani da suka hada da Amurka da hadaddiyar Daular larabawa da kuma Masar wadanda suka kara azama kan matakan diflomasiyya a 'yan watannin baya bayan nan don kawo karshen rikicin.